ABNA24 : Harin da ‘yan bindiga suka ka kai tun a daren Juma’ar da ta gabata ya jawo bacewar yara da dama daga makarantar baya da wasu dalibai da dama da suka tarwatse suka watsu a cikin daji saboda firgici.
Ya zuwa yanzu dai ba’a tantance adadin yawan daliban da suka bace ko aka sace ba sakamakon afkuwar wannnan lamari.
A nasa bangaren shugaban Nigeria Mohammadu buhari ya umarci da a aike da karin dakarun tsaro zuwa inda abin ya faru domin gano da kwato dukkan daliban da ‘yan bindingan suka Sace.
Matsalar tsaro dai na ci gaba da yin kamari a fadin Nigeria musamman a Arewacin kasar duk da kokarin da mahukumta suka ce su na yi na kawo karshen matsalar.
342/